Ferguson ya nuna goyon baya ga De Gea

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Mai tsaron gidan, Manchester United, David de Gea

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya nuna goyon baya ga mai tsaron gidan kungiyar David de Gea duk da cewa kungiyar ta sha kashi a hannun Liverpool a gasar cin kofin FA.

Liverpool dai ta doke Manchester United ne da ci biyu da daya a filin Anfield.

De Gea, ne ya maye gurbin Anders Lindegaard a wasan zagaye na hudu da Kungiyar ta buga, kuma ya dan nuna jinkirin fitowa ya kama kwallo, abun da kuma yasa Daniel Agger ya zura kwallon farko.

Dan wasan United Ji Sung-Park ne ya fanshe kwallo sai kuma Dirk Kuyt ya zura kwallon da ya ba Liverpool nasara dab da a tashi wasan.

"'Yan wasanmu ne suka jawo matsalar da yasa aka zura mana kwallon farko." In ji Ferguson.

"Ba su ba De Gea wurin da zai fito da ya kama kwallon ba."