Villas Boas ya jinjinawa John Terry

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kyaftin din Chelsea, John Terry

Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas ya ce kyaftin din kungiyar John Terry na daya daga cikin 'yan wasan baya da suka kware a duniya.

Terry dai ya lashe gasar Premier uku tare da Chelsea da kuma gasar cin kofin FA hudu a kungiyar.

Villas-Boas, ya ce babu wani tababa a kan kwarewar dan wasan domin babu wani kamarsa a 'yan wasan baya.

"John Terry na daya daga cikin 'yan wasan bayan da su ka kware a duniya, kila ma babu wani kamarsa." In ji Kocin Chelsea a hirar da ya yi da manema labarai.