QPR ta sayi Diakite na wucin gadi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Mali, Samba Diakite

Dan wasan Mali Samba Diakite ya koma kungiyar Queens Park Rangers daga Nancy na wucin gadi har zuwa karshen kakar wasan bana.

Diakite, mai shekarun haihuwa 23, ya baro gasar cin kofin duniya da ake yi a Gabon domin ya kammala sa hannu a yarjejeniyar da ya kullla da kungiyar.

"Dan wasan zai koma QPR na dindin a karshen kakar wasa inda har QPR ta ci gaba da zama a gasar Premier." In ji Kungiyar Nancy a wata sanarwa da ta fitar.

Sabon kocin QPR Mark Hughes ya rika ya sayi 'yan wasa biyu na wucin gadi, wato Nedum Onuoha da kuma Taye Taiwo.