Kocin Zambia ya gargadi 'yan wasansa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Zambia na murnar zura kwallo.

Kocin Zambia Herve Renard ya nuna damuwa game da yadda 'yan wasansa suke kai hari ba kakkautawa.

Kocin ya ce 'yan wasan suna da kwarewa amma basa taka tsan-tsan idan suna wasa.

Zambia dai ta kai matakin wasan dab da kusa dana karshe a gasar cin kofin nahiyar Afrika bayan ta doke Equatorial Guinea da ci daya mai ban haushi a ranar Litinin.

Renard ya jagoranci Zambia a wasan dab da kusa dana karshe a gasar da aka shirya a Angola a shekaru biyun da su ka wuce.

"Idan aka 'yan wasan duka babu wanda zai tsaya a baya. kowa zai nemi da ya kai hari ne." In ji Renard.