Bridge ya koma Sunderland na wucin gadi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wayne Bridge

Sunderland ta sayi dan wasan bayan Manchester City Wayne Bridge na wucin gadi har zuwa karshen kakar wasan bana.

Tsohon dan wasan Chelsea din mai shekarun haihuwa 31, ya takawa City leda sau daya ne a kakar wasan bana, a gasar cin kofin Carling.

Dan wasan bayan dai ya fuskanci matsala ne da kocin kungiyar Mark Hughes.

Dan wasan ya bugawa Ingila wasa sau 36, kuma koma City ne a shekarar 2009.

"Ina fatan Wayne zai taimakawa kungiyarnan saboda kwarewarsa." In ji kocin Sunderland, Martin O'Neil.

"Ina matukar murnar zuwansa kungiyar, saboda 'yan wasanmu da dama na fama da rauni.