Murray ba zai buga gasar Davis Cup

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan Tennis din Burtaniya, Andy Murray

Dan wasan Tennis din Burtaniya, Murray ba zai samu buga gasar cin kofin Davis ba saboda yana jinyar raunin da ya samu a gasar Australian Open.

Burtaniya dai za ta fafata da Slovakia ne a gasar, kuma James Ward da Dan Evans da Colin Fleming da kuma Ross Hutchins ne za su bugawa tawagar Ingila wasa.

"Gaskiya ban ji dadin yadda bazan samu buga gasar Davis Cup ba a bana saboda naji dadin yadda na buga gasar a bara." In ji Murray.

"Amma ganin cewa akwai gasar Olympic a nan gaba, ya kamata in dan huta saboda in dawo da kwarina."

Murray ya kai wasan kusa dana karshe a gasar Australian Open inda Novak Djokovic.