Tevez ya dauka kara a kan Man City

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Carlos Tevez

Dan wasan Manchester City, Carlos Tevez ya daukaka kara ga mahukuntar gasar Premier game da tarar albashinsa na makwanni shida da kungiyar ta ce ya biya.

An ci tarar Tevez fam miliyan daya da dubu dari biyu bayan da aka same shi laifin rashin da'a.

Hukumar Premier za ta sanya rana domin saurara karar da Tevez ya daukaka.

Rigimar da ke tsakanin danwasan da kungiyar City ya sa ya yi asarar fam miliyan tara da dubu dari uku.

Kungiyar Manchester City dai ta ci tarar Tevez ne saboda kocin kungiyar, Roberto Mancini ya yi zargin cewa Tevez ya ki ya taka leda a wasan da kungiyar ta buga da Bayern Munich a gasar zakarun Turai a watan Satumban bara.

Amma Tevez ya musanta hakan inda yace rashin fahimta ne.