Saha ya koma Tottenham a yayinda Pienaar ya dawo Everton

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Louis Saha, ya taka leda na tsawon shekaru uku da rabi a Everton

Louis Saha ya koma Tottenham bayan shekaru uku da rabi a kungiyar Everton.

Shi kuwa tsohon dan wasan Everton din Steven Pienaar dake Tottenham ya dawo kungiyarsa ce ta da ne na wucin gadi, har zuwa karshen kakar wasan bana.

Pienaar ya bar Everton ne a shekarar da ta gabata zuwa Tottenham, kuma ya fuskanci matsaloli wajen samu gurbi a tawagar Tottenham.

"Ina son Louis. Dan wasan ne da ya kware, kuma yana da fahimta sosai." In ji Redknapp.

Shugaban Everton Bill Kenwright da kuma takwararsa na Tottenham wato Daniel Levy sun yi aiki tare ne domin su tabbatar yarjejeniya tsakanin kungiyoyin biyu.