Terry zai gurfana a gaban kotu a watan Yuli

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption John Terry

Kyaftin din Ingila John Terry zai gurfana a gaban kotu a watan Yuli domin amsa zargin laifin wariyar launin fata.

Ana dai zargin dan wasan Chelsea din ne da yin kalamun wariyar launin fata ga dan wasan QPR Anton Ferdinand a wasan da kungiyoyin biyu su ka buga a watan Okutoban bara.

Lauyoyin Terry dai a madadinsa sun ce ba shi da laifi bayan kotun ta saurari karar a ranar Laraba.

A yanzu haka dai dan wasan zai fuskanci shari'a a ranar tara ga watan Yuli, kwanaki tara bayan gasar cin kofin Turai.

A cikin wata sanarwa da Lauyoyin dan wasan su ka fitar, sun ce Mista Terry dai na jiran damar kare kansa.

"Mista Terry ya musanta duk wani zargi na wariyar launin fata, kuma za'a wanke shi a kotu game da wannan zargi."