Wilshere ya kara samun karaya a kafarsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Arsenal Jack Wilshere

Dan wasan Arsenal Jack Wilshere ya samun karaya a yayinda yake jinyar raunin da ya samu a kafarsa ta dama a farkon kakar wasan bana.

An dai yiwa dan wasan Ingilan tiyata a idon sahunsa kuma an yi hasashen cewa zai dawo taka leda a watan Fabrairu.

Amma Arsenal ta bada tabbacin cewa Wilshere ya samu karaya a kafarsa kuma ba zai samu buga wasa ba a kakar wasan bana.

Wilshere bai takawa Ingila leda ba, tun wasan da kasar ta buga da Switzerland, inda su ka tashi biyu da biyu a watan Yunin shekarar 2011.

"Zan tabbatar muka cewa na samu karaya a kafa ta, amma ba inda na samu rauni a baya ba, ina ganin zan murmure a kan lokaci." In ji Wishere a shafinsa na Twitter.