Keshi ya gayyato 'yan wasa talatin

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Stephen Keshi, Kocin tawagar Super Eagles

Kocin tawagar kwallon kafan Najeriya ta Super Eagles ya gayyato 'yan wasa 30 domin zuwa sansanin horo a yayinda kasar ke shirin tunkarar Liberai a wasan sada zumuni a ranar goma sha biyar ga watan Fabrairu

'Yan wasan da kocin ya gayyato sun hada da masu tsaron gida uku, da 'yan wasan baya takwas, da na tsakiya goma shada sannan kuma na gaba guda takwas.

Masu tsaron gida

Chigozie Agbim (Warri Wolves) da Okemute Odah (Sharks FC) da kuma Daniel Akpeyi (Heartland FC).

'Yan wasan baya

Juwon Oshaniwa (Sharks FC) da Osasco Omomo (Sunshine Stars) da Azubuike Egwueke (Warri Wolves) da Godfrey Oboabona (Sunshine Stars) da kuma Gbenga Arokoyo (Kwara United).

sauran sun hada da Uche Oguchi (Heartland FC) da Ahmed Adesope (3SC)da kuma Papa Idris (Kano Pillars).

A 'yan wasan tsakiya

Ossai Uche (Warri Wolves) da Kola Anubi (Sharks FC) da Ejike Uzoenyi (Rangers International) da Bartholomew Ibenegbu da Kingsley Salami da Stanley Ohabuchi (Heartland FC)sai kuma Reuben Gabriel (Kano Pillars).

Sauran kuma su ne, Henry Uche (Enyimba FC) da Solomon Jabason (Akwa United) da Chidi Osuchukwu (Dolphins FC)da kuma Daniel Essien (Niger Tornadoes).

'Yan wasan gaba

Sunday Emmanuel (Enyimba) da Sunday Mba, da Jude Aneke (Warri Wolves) da Izu Azuka (Sunshine Stars) da Barnabas Imenger (Kwara United) da Kabiru Umar (Heartland FC) da Uche Kalu da kuma Ifeanyi Ude (Enyimba FC).