Chelsea da Man U sun tashi uku da uku

Hakkin mallakar hoto AP

Chelsea ta buga kunnenn doki da Manchester United, a yayinda kungiyoyin biyu sun tashi uku da uku da filin Stamford Bridge.

Dan wasan United, Johny Evans ne ya fara zura kwallo a ragar kungiyarsa kafin a tafi hutun lokaci.

Bayan an dawo ne kuma, Juan Mata da David Luiz su ka zura kwallaye biyu cikin mintuna biyar.

Alkalin wasa ya ba Manchester United fenarity biyu wanda Rooney ya zura su a yayinda kuma Havier Hannendez ya zura ta uku.

Chelsea dai ta yi korafi game da bugun fenaritin da Manchester United ta samu a wasan.