Ivory Coast ta kai wasan S/Final

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kyaftin din tawagar, Ivory Coast, Didier Drogba

Ivory Coast ta kai wasan dab da kusa dana karshe a gasar cin kofin Afrika, bayan ta doke daya daga cikin masu saukar baki wato Equatorial Guinea da ci uku da nema.

Kyaftin din tawagar kasar Didier Drogba na daga cikin 'yan wasan da su ka taka rawar gani bayan mai tsaron gida ya tare fenaritin da ya buga.

Drogba dai daga baya ya zura kwallaye biyu a wasan.

Yaya Toure ne ya zura kwallo ta uku a wasan, a bugun falan daya(free kick).