Wenger ya jinjinawa Alex Oxlade-Chamberlain

Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Arsenal boss Arsene Wenger ya jinjinawa matashin dan wasansa saboda yadda ya taka leda a wasan da kungiyar ta buga da Blackburn Rovers.

Arsenal dai ta doke Blackburn ne da ci bakwai da daya, kuma Chambarlian ya zura kwallaye biyu a wasan a yayinda kuma Robin van Persie ya zura kwallaye uku.

"A gaskiya Chamberlain ya nuna kwazo a 'yan watannin nan." In ji Wenger.

Oxlade-Chamberlain dai ya zura kwallonsa ta farko ne a gasar Premier.

Wenger ya sayo dan wasan ne daga Southampton a kan fam miliyan 12 a shekarar 2011.

Kocin na Arsenal ya ce kwalliya ta biya kudin sabulu musamman idan aka lura da yadda dan wasan ke murza leda.