Kocin Zambia ya yaba da 'yan wasansa

Hakkin mallakar hoto a
Image caption Zambia ta doke Sudan ne da ci uku da nema

Kocin Zambia Herve Renard ya jinjinawa 'yan wasansa saboda yadda su ka taka leda a wasan da a wasan dab da kusa dana karshe a gasar cin kofin Afrika.

Zambia dai ta doke Sudan ne da ci uku da nema domin tsallakewa zuwa wasan kusa da na karshe.

"Ba zan iya cewa mun kayatarba, amma gaskiya 'yan wasan sun yi kokari." In ji Renard.

"Na ce akwai miliyoyin 'yan Zambia da ke Turai da Afrika da dama dake kallonsa a talbiji domin kawai na kara musu kwarin gwiwa."