Ferguson ya soki mataimakin alkalin wasa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya soki mataimakin alkalin wasa Darren Cann a wasan da kungiyar ta buga uku da uku da Chelsea.

Ferguson ya ce Cann bai baiwa Man U fenarity ba, bayan da dan wasan bayan kungiyar Gary Cahill ya tade Danny Welbeck.

"Ya kamata da an sallami dan wasan Chelsea daya tun kafin a tafi hutun rabin lokaci." In ji Ferguson.

Ya ce: "Howard Webb ba shi laifi. yana bukatar taimako ne kuma mataimakinsa ya ki ya taimaka."

Manchester United dai ta samu fenarity biyu a wasan, abun da kuma ya kara mata kwarin gwiwa fanshe kwallaye ukun da Chelsea ta zura mata.