FIFA ta ba da gudunmuwa a Masar

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Shugaban Fifa Sepp Blatter

Hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa ta yi kira ga kasashen duniya da su bada gudunmuwa ga iyalan wadanda su ka rasa 'yan uwansu a tarzomar da aka yi a filin wasa a Masar, inda sama da mutane 70 su ka rasa rayukansu.

Fifa ta ce za ta ba iyalan wadanda su ka rasu dala dubu dari da hamsin a matsayin gudunmuwa.

Anyi rikici ne a filin wasa na Port Said, bayan wasan da Al Masry da Alhaly su ka buga.

Fifa ta ce za ta sanya kudin ne a wani asusun bada agaji da kungiyar Al-Ahly ta bude a ranar Lahadi.

Shugaban Hukumar Fifa, Sepp Blatter, ya ce dolene a agazawa wadanda abun ya shafa.