Van der Sar ya gargadi De Gea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mai tsaron gidan Manchester United, David Gea

Tsohon mai tsaron gidan Manchester United, Van der Sar - ya gardadi mai tsaron gidan a yanzu haka da ya fuskanci kalubalen dake gabanshi.

Tsohon mai tsaron gidan kungiyar ya ce dolene ya zage datse yayin ya fara fuskantar matsaloli a lokacin da ya fara bugawa kungiyar wasa.

De Gea, mai shekarun haihuwa 21, ya dawo United ne a kan fam miliyan 18 a daga kungiyar Atletico Madrid.

Dan wasan dai na fuskantar suka daga magoya bayan kungiyar saboda matsalolin da ya fuskanta a watanshi na farko a gasar.

"Dolene ya fuskanci kalubalen dake gabansa saboda an kashe makudan kudade wajen siyansa." In ji Van der Sar.

"Dolene dan wasan ya fuskanci wasu 'yan matsaloli idan ya zo wata sabuwar kungiya da kuma wata gasa ta dabam."