Capello ya yi murabas daga mukamin kocin Ingila

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fabio Capello

Hukumar kwallon Ingila wato FA ta bada tabbacin cewa Fabio Capello ya ajiye aikinsa na kocin Ingila.

Capello dai ya yi murabus ne bayan wata tattaunawa da ya yi da shugaban FA David Bernstein da kuma sakataren hukumar Alex Horne.

Wata sanarwa da Hukumar ta FA ta fitar ta ce: "Muna tabbatar mu ku da cewa Fabio Capello ya ajiye mukaminsa na kocin Ingila."

A ranar Litinin ne dai Capello ya kalubalanci, hukumar ta FA, saboda matakin da ta dauka na tsige Terry daga mukamin kyaftin.

Sanarwar da FA ta fitar ta ce;" Tattaunawar da aka yi da jami'an hukumar da Capello ya ta'alaka ne a kan batun tsige Terry daga mukamin kyaftin da kuma martanin da Capello ya mayar ta kafar yadda labarai."

Hukumar FA din ta ce ta amince da murabus din da kocin ya yi.