Andy Murray ya jinjinawa sabon kocinsa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andy Murray

Shaharren dan wasan, Tennis din Burtaniya, Andy Murray ya yi imanin cewa sabon kocinsa Ivan Lendl ya yi tasiri a takawa rawar da yake yi a kwanan.

Andy Murray wanda shine na daya a fagen Tennis a Burtaniya, kuma na nada Lendl, wanda ya lashe kyautar Grand Slam takwas a matsayin kocinsa a watan Disamban bara.

Murray ya kai matakin wasan kusa da na karshe a gasar Australian Open, inda su ka jimma suna fafatawa tsakaninsa da Novak Djokovic a wasanni biyar.

Andy Murray dai ya ce Lendl ya taka muhimmiyar rawa a wannan wasan.

"Na yi horon kwanaki biyar ne da shi, kafin gasar ta Australian Open, amma sai na ji kawai wasan da nake ya inganta." In ji Murray.