An wanke Redknapp game da zargin kin biyan haraji

Hakkin mallakar hoto
Image caption Harry Rednapp bayan ya fito kotu

Harry Redknapp ya ce a yanzu haka bashi da wata fargaba, bayan da wata kotu a birnin Landan ta wanke shi a kan zargin kin biyan kudaden haraji.

Kocin Tottenham din dai ya musanta zargin karbar garabasa daga tsohon shugaban kungiyar Portsmouth Milan Mandaric daga kudaden siyarda dan wasan kungiyar a wannan lokacin, wato Peter Crouch.

Shima dai Mitsa Mandaric a wanke shi daga zargin kin biyan harajin da ya kai kusan fam dubu biyu ga hukumar karbar haraji a Burtaniya.

Mista Redknapp, wanda ya kusan kuka bayan da ya fito daga kotun, ya ce tun farko ma bai kamata maganar ta zo bagan kotu ba.

Ya yiwa iyalansa godiya da kuma magoyan bayan kungiyar Tottenham, saboda irin kwarin gwiwar da su ka bashi a lokacin da ake shari'ar.

Binciken da aka yi a kan Redknap ya kai tsawon shekaru biyar, kuma ya kashe wajen miliyan takwas wajen biyan lauyoyinsa.