Zambia ta ba Ghana mamaki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Zambia, su na murnar zura kwallo

Emmanuel Mayuka ya taso daga benci, kuma ya zura kwallon da ya ba kasar Zambia nasara a kan Ghana a wasan kusa da na karshe da kasashen biyu su ka buga a gasar cin kofin Afrika.

Zambia dai ta zura kwallon ne ana sauran mintuna goma sha biyu kafin a tashi wasan.

Dan wasan Ghana, Asamoah Gyan ya zubar da fenaritin da kasar ta samu kafin a tafi hutun lokaci.

Ghana dai ta kammala wasan ne da 'yan wasan goma saboda an sallami Derek Boateng bayan an nuna mishi katin gargadi na biyu.

Zambia dai ba ta taba lashe gasar cin kofin Afrika ba, amma ta buga wasan karshe har sau biyu. A shekarar alif dari tara da casa'in da tara ne dai kasar ta buga wasan karshe da Najeriya inda Najeriya ta yi galaba a kan ta.

Ghana wadda ta buga wasan karshen a shekarar 2010 ba ta lashe gasar na tsawon shekaru talatin kenan.