FA za ta tattauna a kan wanda zai gaji Capello

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Hukumar FA, David Bernstein

Hukumar kwallon Ingila wato FA ta ce za ta tattauna a ranar Juma'a domin zabar wanda zai maye gurbin Fabio Capello, amma za ta fi maida hankali ne kan kocin mai jin Ingilishi kuma dan Burtaniya.

Shugaban Hukumar, ya ce hukumar na son maye gurbin kocin ne cikin gaggawa, amma ya ki ya ce uffan game da jita-jitan da ake yi cewa hukumar na zawarcin Harry Redknapp.

"Zamu yi abun da ya dace, kuma zamu fito da jerin sunayen wadanda muke so." In ji Bernstein.

Mataimakin kocin Ingila, Stuart Pearce ne zai jagoranci kasar a wasan sada zumuncin da za ta buga da Holland a ranar 29 ga watan Fabrairu.