Muna son Tevez amma albashinsa ya yi yawa

tevez Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Carlos Tevez

Kocin Paris Saint-Germain Carlo Ancelotti ya ce zai so ya sayi Carlos Tevez, amma kuma albashin dan Argentina din shine matsala.

Dan kwallon mai shekaru 27 wanda har yanzu dan wasan Manchester City ne,kungiyoyi kamarsu AC Milan da Inter Milan da kuma PSG sun nuna sha'awarsu akansa amma sai cinikin bai yiwu ba.

Ancelotti ya ce"Mun tattauna da wakilansa, mun nemi sayansa amma sai muka kasa cimma yarjejeniya".

Kocin City Roberto Mancini ya saka suna Tevez a cikin jerin 'yan wasa 25 da zasu bugawa kulob din wasa har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Kocin mai shekaru 52 ya ce PSG zata jira har zuwa karshen kakar wasa ta bana don watakila ta siye shi.

Karin bayani