Osaze ya zura kwallaye 3 a nasarar West Brom

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Peter Osaze Odemwingie

Dan wasan Najeriya da ke takawa kungiyar West Brom leda Peter Osaze Odemwingie ya zura kwallaye uku a wasan da kungiyarsa ta West Brom ta doke Wolves da ci biyar da daya.

Odemwingie ne ya zura kwallon karfo sannan kuma ana daf da tafiya hutun rabin lokaci ne Steven Fletcher ya fanshewa Wolves.

Bayan an dawo hutun ne Jonas Olsson ya zura kwallo sannan Odemwingie ya zura biyu kafin Keith Andrews ya zura kwallo ta biyar a ragar Wolves.

Wannan dai shine karo na shida a jere da Wolves ta sha kashi a gida a gasar ta Premier.