Suarez ya bada hakuri saboda kin gaisawa da Evra

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Luis Saurez da Patrice Evra basa jituwa

Dan wasan Liverpool Luis Suarez ya bada hakuri saboda kin gaisawa da ya yi da dan wasan Manchester United, Patrice Evra a wasan da kungiyoyin biyu su ka buga a gasar Premier ta Ingila.

Manchester United dai ta doke Liverpool ne da ci biyu da daya a wasan da su ka buga a ranar asabar.

An dakatar da Suarez na tsawon wasanni takwas bayan da aka same shi da laifi yiwa Patrice Evra, kalamun wariyar launin fata a wasan da kungiyoyin biyu su ka buga a watan Okutoban bara.

Amma a wasan da aka buga a filin Old Trafford, Suarez ya ki ya mikawa Evra hannu su gaisa a lokacin da 'yan wasan ke gaisawa kafin a fara wasa.

Wannan lamari dai ya fusata, Evra.

Wata sanarwa da Suarez ya buga a shafin Liverpool ya ce: "Na yi magana da kocina, [Kenny Dalglish] tun bayan wasanmu a filin Old Trafford, kuma na amince cewa banyi dai-dai."

"Ba kawai na ba kocin kunya bane har ta ma da kungiyar. Gaskiya abun da nayi bai dace ba, kuma nayi nadama da abun da ya faru.

"Ya kamata in baiwa Patrice Evra hannu mu gaisa, kuma a yi hakuri."