An gurfanar da Emenike a gaban kotu a Turkiyya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan Najeriya, Emmanuel Emenike zai shiga kotu

Wata Kotu a Turkiyya ta fara shari'ar mutane 90 da ake da hannu wajen yin coge a harkar kwallon kafa a kasar, daga cikin har da dan Najeriya Emmanuel Emenike.

Emmanuel Emenike wanda ya ke kungiyar Fernabace leda a da na cikin 'yan wasan 14 da kotun ke tuhuma.

A yanzu haka dai Emenike na kungiyar Spartak Moscow ne a rasha kuma bai ta ba takawa Fenerbahce leda ba kafin ta siyarsa da shi.

Ana dai zargin Emenike ne da amincewa da kin takawa kungiyarsa ta Karabukspor leda a wasan da ta buga da Fernabace, saboda Fernabace ta yi alkawarin za ta siye shi.

Amma kungiyar Karabukspor ta musanta zargin, inda ta ce Emenike bai buga wasan bane saboda ya samu rauni mako daya kafin wasan, kuma yana da takardun asibiti da ke nuni da hakan.

Idan har an samu Emenike da laifi za'a iya daure shi a gidan kaso na tsawon shekaru uku.