Goran Stevanovic zai san makomarsa a mako mai zuwa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Tawagar kasar Ghana

Hukumar kwallon kafan Ghana za ta tattauna a mako mai zuwa game da makomar kocin tawagar kasar Goran Stevanovic, bayan da kasar ta zama ta hudu a gasar cin kofin Afrika da aka kammala a jiya.

Kocin dai zai mika cikakken rahoto ga kwamitin gudanarwa na hukumar kan yadda Ghana ta tafiyar da ayyukanta a yayinda ka halarci gasar.

Kwamitin dai zai tattauna a ranar Talata mai zuwa kuma zai bayyana matakin da ya dauka a kan kocin a ranar 22 ga watan Fabrairu.

Stevanovic na so ya ci gaba da aiki da Ghana, amma akwai manya jami'an hukumar kwallon kafan kasar da dama dake nema a sallame shi.

Saura dai shekara daya kwantaragin kocin ya cika wanda ke karbar kusan dala dubu hamsin a wata.