Mancini ya wulakanta ni kamar kare- Tevez

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Carlos Tevez

Carlos Tevez zai dawo takawa Manchester City leda duk da cewa ya zargin kocin kungiyar Roberto Mancini da wulanta shi kamar kare.

Dan wasan bai takawa City leda ba tun da Mancini ya zarge shi da kin shigowa wasan da kungiyar ta buga da Bayerm Munich a watan Satumban bara.

Dan wasan ya yi zargin cewa Mancini ya zage shi, amma a shirye yake ya dawo taka leda; " A shirye nake na dawo taka leda domin in taimakawa kungiyar ci gaba da samun nasara."

A baya dai Mancini ya ce dan wasan ba zai kara taka masa leda, amma a yanzu haka ya sauya matsaya inda ya ce zai bari dan wasan ya dawo taka leda amma idan ya yi nadama.

Har yanzu dai City ba ta mayarda martani ba game da zargin da Tevez ya yi.