Wilshere zai dawo nan da wata daya- Wenger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jack Wilshere

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce yana fatan dan wasansa Jack Wilshere zai dawo nan da wata daya.

An dai yiwa dan wasan tiyata a idon sahunsa a watan Satumban bara daga baya kuma ya samu targade a kafarsa ta dama a lokacin da ya ke kokarin murmurewa.

Wenger ya ce: "Jack zai dawo nan da wata daya, idan komai ya tafi daidai."

Har wa yau dai, kungiyar ta Arsenal za ta yi rashin dan wasan bayan ta Per Mertesacker na tsawon wata daya, bayan raunin da ya samu a wasan da kungiyar ta buga da Sunderland.

Wilshere dai bai buga wasa ba a kakar wasa bana bayan raunin da ya samu a wasannin share fage na sada zumunci da Arsenal ta buga a kungiyar New York Red Bulls a watan Yulin bara.

Wenger dai ya ce zai yi taka tsan-tsan wajen ganin dan wasan ya murmure garau domin dawo taka leda.