AC Milan ta jikawa Arsenal gari

Hakkin mallakar hoto 1

Kungiyar AC Milan dai ta lallasa Arsenal da ci hudu ba ko daya a gasar zakarun Turai, a tattakin da Arsenal ta kai filin sansiro.

Dan kasar Ghana, Kevin Prince Boateng ne ya fara zura kwallon farko, ana minti 15 da fara wasan.

Sannan kuma an kusan tafiya hutun rabin lokaci ne dai, Robinho ya zura ta biyu.

Har wa yau ana dawowa hutun rabin lokaci ne dan wasan ya zura kwallo ta uku a ragar Arsenal.

AC milan dai ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida ana saura minti goma sha daya a tashi wasan, bayan da Djourou ya tade Ibrahimovic. dinne kuma ya taso ya zura kwallon.