Zambia ta shiga cikin sahun kasashe 50 a kwallon kafa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Tawagar Zambia

Zambia wadda ta lashe gasar cin kofin Afrika ta hau sama zuwa matsayi na 43 a jerin kasashen da su ka kware wajen taka leda da Fifa ta fito da shi.

Tawagar Chipolopolo ta Zambia ta doke Ivory Coast a babban birnin Gabon, wato Libreville inda ta lashe kofin Afrika a karon farko a ranar Lahadi.

Wannane karo na farko da kasar ta dago sama cikin shekaru 11 har ma ta shiga cikin kasashen 50 da su ka kware a harkar tamoula.

Har yanzu dai Ivory Coast ce ta daya a Afrika amma ta kara matsayi a duniya da mataki uku inda a yanzu haka itace ta 15.

Mali wadda ta zo ta uku a gasar cin kofin Afrikan ta tason sama da mataki 25, inda a yanzu haka itace ta 44 a duniya.

Gabon wadda ke daya daga cikin kasashen da ta daukin nauyin bakuncin gasar ne ta dago daga mataki na 91 zuwa 45.

Ita ko Equatorial Guinea ta daga ne daga matakin 151 zuwa 110.