Zenith ta doke Benfica da ci 3-2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zenit St Petersburg ta doke Benfica da ci uku da biyu

Roman Shirokov ya taimakawa kungiyarsa ta Zenit St Petersburg da kwallaye biyu a nasarar da kungiyar ta yi a kan Benfica a gasar Zakarun Turai.

Zenith dai ta doke Benfica ne da ci uku da biyu.

Benfica wadda ta yi tattaki zuwa Rasha ce ta fara zura kwallon farko, ta kafar Maxi Pereira.

Ana cikin wasan ne kuma Shirikov ya zura kwallonsa ta farko wa Kungiyar a yayinda kuma Sergei Semak ya sanya kungiyar a gaba.

Oscar Cardozo dai ne yanshewa Benfica kafin Shirokov ya zo ya zura kwallon da ya ba Zenith nasara a wasan.