Kashin da muka sha ya samu cikin kaduwa- Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kocin Arsenal Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya bayyana kashin da kungiyarshi ta sha a hannu AC Milan a matsayin wata annoba wadda ta sanya kungiyar cikin kaduwa.

AC Milan dai ta doke Arsenal ne a filin sansiro da ci hudu da nema a gasar zakarun Turai a daren ranar Laraba.

Wenger ya amince cewa kungiyarsa ta fita daga gasar zakarun Turai, kuma kashin da ta sha, shine mafi muni a Turai.

Kocin ya ce: "Ba'a duniyar mafarki mu ke ba, da wuya mu iya tsallake zuwa zagaye na gaba. Abun da ya fito zahiri shine mun fita a gasar."

"Mun yi kuskure, kuma mun dandana kudar mu."

Ya kara da cewa: "Babu sanda muka yi wani abun a zo a gani a wasan, bamu taka rawar gani ba.