Carroll na farin cikin takawa Liverpool leda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Carroll

Dan wasan gaban Liverpool Andy Carroll ya ce yana matukar farin ciki da zamansa a kungiyar.

Tun da dan wasan ya koma Liverpool daga Newcastle a watan Junairun 2011 a kan fam miliyan 35, dan wasan ya zura kwallaye takwas ne kawai a wasanni 40 da ya bugawa kungiyar.

"Ina ganin, ina taka rawar gani. Na fara zura kwallaye, kuma ina ganin komai ya fara tafiya dai-dai." In ji Carroll.

"Ina murna kuma ina da kwarin giwa a yanzu haka."

Liverpool dai za ta buga wasan karshen a gasar cin kofin Carling da Cardiff a ranar Lahadi.