BBC navigation

Gyan zai dawo taka leda a watan Yuni- GFA

An sabunta: 20 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 18:22 GMT

Asamoah Gyan

Hukumar kula kwallon Ghana-GFA ta ce Asamoah Gyan zai dawo takawa kasar leda, bayan ta lallashe shi da ya sauya matakin yin murabus din da ya ce ya yi a karshen makon da ya gabata.

Mataimakin shugaban hukumar kwallon kasar, Jordan Anagbla ya ce yana da kwarin gwiwa cewa dan wasan zai dawo taka leda a wasan share fage da kasar za ta buga da Lesotho da kuma Zambia a watan Yuni.

Asamoah Gyan dai ya amince cewa har yanzu bai gama murmurewa ba daga koma bayan da ya fuskanta a gasar cin kofin duniyar da aka shirya a shekara ta 2010.

Dan wasan dai ya barar da fenaritin da ya kamata ya kai Ghana wasan kusa da na karshe a gasar cin.

Dan wasan dai a yanzu haka ya yi murabus daga tawagar kwallon kasar, bayan ya sake barar da fenariti a wasan kusa dana karshe da Ghana ta buga da Zambia a gasar cin kofin Afrika da aka shirya a bana.

Wannan dai ya jawo mashi suka sosai daga 'yan kasar da dama saboda rashin nasarar da kasar ta fuskanta a gasar.

"Gaskiya a yanzu haka bani da kwarin gwiwa," In ji Gyan.

"Hankali na ya ki kwantawa tun bayan da na barar da fenariti biyu da ya kamata ya taimakawa kasa ta."

"Ban gama murmurewa daga abun da ya fara a gasar cin kofin duniya a shekarar 2010 kuma yanzu ga na shekarar 2012."

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.