Kan Chelsea a hade ya ke- Sturridge

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daniel Sturridge

Dan wasan Chelsea, Daniel Sturridge ya nace cewa babu rashin jituwa a kungiyar a daidai lokacin da kungiyar ke shirin haduwa da Napoli a gasar zakarun Turai a ranar Talata.

Akwai dai 'yan wasan kungiyar da basu amince da dabarun Andre Villas-Boas ba, kuma kocin ya musanta rahotanin da ke cewa Didier Drogba ya yi jawabin kara karfin gwiwa ga manema labarai a wasan da kungiyar ta buga da Birmingham a karshen makon da ya gabata.

"Duk daya muke, kan mua hade yake babu rashin jituwa tsakanin mu." In ji Sturridge a hirar da ya yi da gidan talbijin din Chelsea.

Chelsea dai ba ta lashe wasa ko daya ba tun daga ranar 28 ga watan Junairu, kuma basu taba fuskantar koma bayan da suke samu a yanzu haka ba, tun da Roman Abramovich ya sayo kungiyar a shekara ta 2003.