Za mu murkushe wariyar launin fata a kwallon kafa- Cameron

Image caption David Cameron

Pira Ministan Burtaniya, David Cameron ya yi alkawarin murkushe wariyar launin fata a harkar kwallon kafa a wani taron da aka kaddamar na yaki da wariyar launin fata a fadar gwamnatinsa.

David Cameron, wanda ke tare da manyan 'tsaffin 'yan wasa kamar su Graeme Le Saux da John Barnes, ya yaba da ci gaban da aka samu wajen yaki da wariyar launin fara a harkar wasanni a Burtaniya.

Har wa yau ya amince cewa dabi'ar ta fara dawowa harkar wasanni a Burtaniya.

Mista Cameron ya ce yana da kwarin gwiwa harkar wasanni za ta magance matsalar wariyar launin fata.