Carlos Tevez ya bada hakuri

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Carlos Tevez

Dan wasan Manchester City Carlos Tevez ya bada hakuri saboda rashin da'ar da ya nuna na kin shigowa wasa, kamar yadda kocinsa ya bukata.

Tevez dai ya ki shiga wasa ya taka leda ne a wasan da Bayern Munich ta doke City da ci biyu da nema a gasar zakarun Turai a bara.

Wannan dai ya jawo takkadama tsakanin kocin da kungiyar abun da kuma yasa kungiyar ta ci tararsa.

Tevez dai ya dawo kungiyar a makon daya gabata bayan ya yi kaura daga kungiyar na kusan watanni uku.

Kocin City Roberto Mancini ya ce zai tafi da shi muddin ya nemi ahuwa.

Shima dai Tevez din ya janye karar da ya shigar a kan kungiyar saboda matakin da ta dauka a kan shi.