Tevez zai dawo takawa City leda - Mancini

Hakkin mallakar hoto g
Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini, ya ce ya amince da ahuwar da Carlos Tevez ya nema, kuma dan wasan zai dawo taka leda nan da makwanni biyu zuwa uku.

Tevez dai ya bar kungiyar na tsawon watanni uku ba tare da izini ba, bayan dambarwar da ta kaure tsakaninsa da kocin kungiyar.

Tevez dai ya dawo kungiyar ne a makon daya gabata, kuma ya nemi ahuwa daga kungiyar da magoya bayanta.

Mancini dai ya ce ya kamata dan wasan ya yi horo sosai, kafin ya dawo taka leda gadan-gadan.