Andre Villas-Boas ya kare 'yan wasan da ya zaba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Andre Villas-Boas

Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas ya kare matakin da ya dauka na ajiye wasu manyan yan wasansa a wasan da kungiyarsa ta sha kashi a hannun Napoli da ci uku da daya a gasar zakarun Turai.

Kocin dai bai sanya Ashley Cole da Michael Essien da Frank Lampard da kuma Fernando Torres a cikin 'yan wasa 11 da su ka fara wasan.

"Zaku iya samun naku ra'ayin, amma ni agani na na zabi 'yan wasan dasu ka dace." In ji Villas-Boas.

"Zan duba inda muka yi daidai da inda muka yi kuskure, sai mu san inda za'a gyara. Zai yiwu muyi nasara duk da cewa dai an doke mu da ci 3-1."

An dai sanya Cole a wasan ne ana minti 12 bayan da Bosingwa ya samu rauni.

Daga baya kuma aka sanya Essien da Lampard, bayan an zura kwallaye ukua ragar kungiyar.