Pearce ya nuna kwadayin jagorantar Ingila a Euro 2012

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Ingila na wucin gadi, Stuart Pearce

Kocin Ingila na wucin gadi Stuart Pearce ya ce zai iya jagorantar kasar zuwa gasar cin kofin Turai da za'a shirya a kasar Poland da Ukraine.

Kocin wanda har wa yau shi ke jagorancin tawagar 'yan kasa da shekaru 21 ya gayyato Fraizer Campbell da kuma Tom Cleverley cikin 'yan wasan kasar da za su buga wasan sada zumunci da Holland a filin Wembley a ranar Laraba mai zuwa.

"Ina da gogewa a manyan gasa irin wannan, kuma idan suna bukatata, zan karbi aikin." In ji Pearce.

A baya dai kocin ya nisanta kansa da karbar aiki a matsayin na dindindin bayan da aka Sallami Fabio Capello a watan da ya gabata.

"Wannan aikin na bukatar wanda ya kware, kuma ina da gogewar da zan iya daukar aikin a yanzu haka." In ji Pearce.

Kocin Tottenham, Harry Redknapp dai na daya cikin wadanda ake hasashen za su jagoranci tawagar ta Ingila, amma Pearce ya ki ya ce uffan game da maganar.