Kalubalen da Chelsea ke fuskanta laifi na ne- Villas Boas

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya ce 'yan wasansa ba su da laifi game da koma bayan da kungiyar ke fuskanta, inda ya daurawa kansa laifi game da rashin nasarar da kungiyar ta fuskanta a gasar zakarun Turai.

Ya kara da cewa baya bukatar goyon bayan 'yan wasansa a yayinda yake kokarin farfado da kungiyar bayan rashin nasarar da ta fuskanta.

Villas-Boas ya kara da cewa: "Yan wasan basa daukan laifi.

"Manyan 'yan wasa ne, kuma sun san abun da suke yi. Mutum daya ne kuma za'a iya daurawa laifi kuma ni ne."

Ya kara da cewa: "Kungiyar ta fi kowa mahimmaci, saboda haka ko ina da goyon baya ko bani da shi ya kamata a maida hankalin wajen gyara abubuwa."

Kocin ya ce mai kungiyar Roman Abramovich ya nuna rashin jin dadinsa game da 'yan wasan da ya yi amfani dasu a kashin da kungiyar ta sha a hannun Napoli.

Villas-Boas ya kara da cewa: "Na yi magana da na kusa da shi. Ya nuna rashin jin dadinsa, kuma ya yi tambaya ya aka yi, kuma mun yi bayani."