An nada Connor a matsayin kocin Wolves

 Terry Connor
Image caption Terry Connor da Mick McCarthy

Kungiyar Wolves ta daukaka matsayin mataimakin kocinta Terry Connor zuwa matsayin babban koci har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Kulob din ya kori Mick McCarthy a ranar 13 ga watan Fabarairu bayan sun sha kashi a wajen abokan hammayarsu West Brom daci biyar da daya.

Wolves ta koma kan Connor mai shekaru 49, bayanda Walter Smith, Alan Curbishley da kuma Brian McDermott suka ce ba zasu karbi mukamin ba.

Mai kulob din Wolves, Steve Morgan ya ce "wannan matakin yayi dai dai saboda 'yan wasa na goyon bayansa".

Connor ya kasance tare da Wolves na tsawon shekaru 13 kuma ya yi aiki a karkashin masu horadda 'yan was a hudu, amma kuma wannan ne karon farko da ya zama babban koci.

Karin bayani