Lampard ya ce akwai jikakkiya da Villas-Boas

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan Chelsea, Frank Lampard

Dan wasan Chelsea, Frank Lampard ya amince cewa akwai jikakkiya tsakaninsa da kocin kungiyar Andre Villas-Boas.

Amma bayan nasarar da Chelsea ta yi akan Bolton a ranar asabar da ci uku da nema, dan wasan ya ce zai ci gaba sadaukar da kai a kungiyar.

Lampard ya ce: "Ina ganin daga waje dai an san akwai rashin jituwa tsakaninmu. Abun da za'a maida hankali shine a kan kungiyar ba wai dangantakar mu ba.

Shi kuwa Villas-Boas ya jinjinawa Lampard ne bayan nasarar da Chelsea ta yi a kan Bolton amma kocin ya ce duk da cewa dai dan wasan ya taka rawar gani, ba wai tabbas bane zai rika taka leda a koda yaushe.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 33 bai buga wasanni Premier guda biyun da su ka wuce da kuma wasa da Napoli a gasar zakarun Turai.

Amma dan wasan ne ya jagoranci Chelsea a wasan da ta buga da Bolton inda kuma ya zura kwallo ta 150 a gasar Premier.