Arsenal ta yi gaggarumar riba wajen siyarda 'yan wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Arsenal na murnar zura kwallo

Rahotanni sun ce kungiyar Arsenal da ke taka leda a gasar Premier ta Ingila ta samu gaggarumar riba da ya kai fam miliyan hamsin bayan ta siyar da wasu manyan 'yan wasanta.

Kungiyar ta samu riba ne na tsawon watanni shida a karshen watan Nuwamban bara, a maimakon faduwar da ta yi na fam miliyan shida da dubu dari daya a shekarar 2010.

Kungiyar dai ta samu fam miliyan arba'in da daya da dubu dari shida ne wajen siyarda 'yan wasanta daga ciki har da Samir Nasri da Cesc Fabregas.

Arsenal ta fuskanci matsaloli saboda rashin manyan 'yan wasa a kakar wasan bana, amma a karshen makon da ya gabata kungiyar ta doke Tottenham Hotspur da ci 5-2.

Kudaden ajiyar kungiyar ya karu ne daga fam miliyan 110.4 zuwa fam miliyan 115.2.