Pearce ba zai bayyana sunan kyaftin din Ingila ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kocin wucin gadi na Ingila, Stuart Pearce

Kocin wucin gadi na Ingila, Stuart Pearce ya ce ba zai bayyana sunan sabon kyaftin din tawagar kasar ba, sai wasu 'yan sa'o'i kafin wasan sada zumunci da kasar za ta buga da Holland a ranar Laraba.

An yi dai hasashen cewa kocin zai bayyana wanda zai jagoranci kungiyar a wata hira da manema labarai a ranar Talat, amma sai yaki yin hakan.

Dan wasan Liverpool Steven Gerrard da mai tsaron gidan Manchester City, Joe Hart na daga cikin wadanda ake ganin za su iya samu mukamin.

"Zan bayyana sunan kyaftin a lokacin da zan bayyana sunayen 'yan wasan. Akwai 'yan wasa da dama da su ka cancanci a basu mukamin, amma na riga na yanke shawarar wanda zan ba." In ji Pearce.

Dan wasan Tottenham, Scott Parker da na Manchester City James Milner ne cikin 'yan wasan da ake ganin kocin na iya zaba.