Stevanovic zai jagorancin Ghana a wasa da Chile

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Goran Stevanovic

Kocin Ghana Goran Stevanovic ya samu bizar shiga Amurka kuma shine zai jagoranci tawagar kasar a wasan sada zumunci da Chile.

Yawancin dai 'yan wasan kasar dai sun bar Accra ne a ranar Lahadi, amma an dakatar da Stevanovic da 'yan wasa biyu wato Emmanuel Baffour da kuma Richard Mpong.

Yanzu dai dukkansu uku sun samu bizar tafiya.

Wasan da Ghana za ta buga da Chile na iya zama wasa na karshe da Stevanovic zai jagoranci tawagar Black Stars.

A mako mai zuwa ne dai Hukumar kula da kwallon kafa a Ghana za ta dauki mataki game da kocin.

Ghana dai ta kare ne a matsayi na hudu a gasar cin kofin Afrika da aka kammala inda Guinea ra fidda ta a wasan kusa da na karshe.