Villas-Boas ya amince cewa yana zaman dar-dar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Villas-Boas

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas, ya ce yana zaman dar-dar ne a kungiyar saboda a za'a iya sallamansa idan kungiyar ta ga dama.

A baya dai Villas-Boas ya ce yana da goyon bayan mai kungiyar wato, Roman Abramovich dari bisa dari.

Amma a wata hira da yayi da wani gidan rediyo a Portugal, ya ce za'a iya sallamarsa kamar yadda aka sallami Carlo Ancelotti a bara.

"Abu biyu ne zai iya faruwa, ko dai a bar ni na ci gaba da sauyi a kungiyar ko kuma a bar kungiyar yadda ta saba taka leda a baya." In ji Villas-Boas.

"Basan ko gobe zan wuce ba, ko kuma nan da shekaru biyu."

Chelsea dai a yanzu haka tana maki 17 ne a bayan mai jagoranci a gasar Premier wato Manchester City.

Kungiyar na fuskantar kalubalen a gasar zakarun Turai, bayan da Napoli ta doke ta a bugun farko da ci uku da daya.