An dakatar da Chisora daga demben boxing

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dereck Chisora

Hukumar kula da wasan demben boxing ta WBC ta dakatar da Dereck Chisora har illa mashallah saboda dabi'ar da ya nuna bayan demben da ya yi da Vitali Klitschko.

Chisora wanda zakaran dembe ne a Burtaniya, ya yi wata dambarwa ne da David Haye a dakin ganawa da manema labarai bayan demben da yayi da Klitschko.

Harwa yau, Chisora ya mari Klitschko kafin demben sannan kuma ya tofawa dan uwan Klitschko, Wladimir ruwa.

Hukumar WBC ta ce; "Dabi'ar da dan wasan ya nuna shine mafi muni a wasan demben boxing."

Hukumar dai ta nemi Chisora, da ya nemi magani sannan za ta duba ko za ta iya dage dakatarwar da aka yi mishi.